• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Gwamnan Kano Ya Sanya Ranar Komawa Jam’iyyar APC

aksam by aksam
January 25, 2026
Reading Time: 2 mins read
0
Home SIYASA
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Ya Koma Jam’iyyar National Democratic Congress (NDC) A Hukumance; Inda Ya Karɓi Katin Zama Mamba Na Jam’iyyar

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Ya Fice Daga Jam’iyar PDP

Wasu Dalilin Da Suka Sa Kwankwaso Ke Shirin Ficewa Daga Jam’iyyar ADC

Daga: Hassan Umar Gwammaja

A gobe litine 26 ga watan January, 2026 hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu kuma ya aikowa Aksam media ranar Lahadi.

Idan Za a iya tunawa Gwamna Yusuf ya taba shiga jam’iyyar APC ne a shekarar 2014, lokacin da ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar domin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, sai dai daga bisani ya janye wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Sanarwar ta bayyana cewa bayan shafe shekaru yana harkokin siyasa a jam’iyyu daban-daban, ciki har da NNPP, inda a halin da ake ciki harkokin mulki, haɗin kan ƙasa da kuma buƙatar ci gaba sun sa ya yanke shawarar komawa APC, wadda ya bayyana a matsayin jam’iyya mai tsari da gogewa wajen tafiyar da mulkin dimokuraɗiyya.

Gwamna Yusuf ya ce komawarsa APC za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da ta tarayya, da kawo ci gana jihar Kano .

Ya ƙara da cewa matakin zai taimaka wajen ƙarfafa kwanciyar hankali da haɗin kan siyasa a jihar.

A ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026, ana sa ran gwamnan zai yi rajistar shiga jam’iyyar APC a hukumance a Kano tare da mambobi 22 na Majalisar Dokokin Jihar Kano, mambobi takwas na Majalisar Wakilai da kuma shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Haka kuma ana sa ran zai ƙaddamar da shirin rajistar APC ta yanar gizo (e-registration) a faɗin jihar.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Ƙasashen Turai sun fara maye gurbin manyan kamfanonin fasaha na Amurka da na cikin gida

Next Post

Ɗan Kwankwaso, Kwamishinan Wasanni Ya Yi Murabus Daga Gwamnatin Abba Labari Yusuf

aksam

aksam

RelatedPosts

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Ya Koma  Jam’iyyar National Democratic Congress (NDC)  A Hukumance; Inda Ya Karɓi Katin Zama Mamba Na Jam’iyyar
SIYASA

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Ya Koma Jam’iyyar National Democratic Congress (NDC) A Hukumance; Inda Ya Karɓi Katin Zama Mamba Na Jam’iyyar

by aksam
May 3, 2026
Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Umarci  Duk Masu Riƙe Da Mukaman Siyasa Dake Da Niyyar Tsayawa Takara Dasu Yi Murabus Kafin Ranar Juma’a 24 ga Watan Afrilu 2026
SIYASA

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Ya Fice Daga Jam’iyar PDP

by aksam
May 2, 2026
Ba Za Mu Bawa Kwankwaso Tikitin Takarar Shugabancin Kasa A Jam’iyyarmu— NNPP
SIYASA

Wasu Dalilin Da Suka Sa Kwankwaso Ke Shirin Ficewa Daga Jam’iyyar ADC

by aksam
May 2, 2026
Masu Ruwa Da Tsaki A  APCn Kano Sun Amince Da Takarar Abba da Tinubu Karo Na Biyu A Zaɓen 2027
SIYASA

Masu Ruwa Da Tsaki A APCn Kano Sun Amince Da Takarar Abba da Tinubu Karo Na Biyu A Zaɓen 2027

by aksam
May 1, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Yanzu-yanzu Tinubu na gudanar da taro da shugabannin tsaro na Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirinta Na Siyyar Da Buhun Shinkafa Akan Naira Dubu 40,000

August 8, 2024
Rikicin Cikin Gida Da Ya Dabaibaye Jam’iyyar APC A jihar Kano Ya Sake Daukar Sabon Salo

Rikicin Cikin Gida Da Ya Dabaibaye Jam’iyyar APC A jihar Kano Ya Sake Daukar Sabon Salo

April 21, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media