• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Gwamnan Kano, Abba Kabir, ya fitar da mata takwas daga gidan Yari

aksam by aksam
May 10, 2025
Reading Time: 1 min read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir ya biyawa wasu mata takwas kudaden bashin da ake binsu wanda ya yi sanadiyyar shigar su gidajen gyaran hali da tarbiyya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar tace gwamnan ya biya kudin ne yayin wata ziyarar bazata da ya kai gidajen gyaran hali da tarbiyya na Goron Dutsen da Janguza.

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

Gwamna Yusuf wanda ya jajantawa wadanda ke daure a gidan gyaran halin sakamakon ibtilain da suka tsinci kawunan su a ciki, yace ya kai ziyarar ne domin ganewa idonsa irin yanayi da kuma rayuwar da suke yi a gidan gyaran hali.

Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda yace gwamnati zata samar da tsarin da zata biya kudaden tarar da aka yankewa wasu daga cikin daurarrun domin su tuba su koma ga iyalansu yace gwamnatinsa zata taimaka musu ta hanyar koyar dasu sana’oin dogaro da kai da inganta kula da lafiya da iliminsu.

Gwamna Yusuf ya gargadesu da su yi amfani lokutan zamansu a gidan gyaran halin, wajen gyara dabi’u da halayensu, Yana mai cewa gwamnati zata samar da tsarin koyar dasu dasu ilimin addini dana zamani.

Ya yi amfani da ziyarar inda ya kewaya dukkanin sassan gidan kama daga wajen dafa musu abinci da wajen kwanciyarsu tare da duba irin nau’ikan abincin da ake basu.

Kana ya ja hankalin daurarrun da su yawaita tuba ga Allah tare da Neman yafiya daga iyayensu da kuma yi musu addu’a.

Daya daga cikin daurarrun wanda ya shafe sama da shekaru 30 a daure ya godewa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan ziyara da ya kawo musu.

Wannan ziyara ta gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ta zo daidai lokacin da ake yada wasu korafe-korafe kan yanayin rayuwar da fursunoni su ke ciki a wannan kasa.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Next Post

Gwamnan Borno ya haramta siyar da Man fetur a wata karamar hukuma a jihar karanta Dalili

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan
LABARAI

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

by aksam
May 4, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano
LABARAI

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

by Khadija Maitaya
May 4, 2026
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A  Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga  Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC
LABARAI

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC

by aksam
May 3, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Tsananin rayuwa ta sa wata baiwar Allah ciyar da yayan ta da dusar kaji

Tsananin rayuwa ta sa wata baiwar Allah ciyar da yayan ta da dusar kaji

August 15, 2024
Sakacin Jami’an Tsaro Ne Ya Sa Masu Zanga-Zanga Su Ka Yi Barna A Jihar Kano:–  Sarkin Kano Na Goma 16 Muhammadu Sunusi ll

Zargin Karya Dokar Hawan Sallah: Rundunar ‘Yansanda Ta Kasa Ta Aikewa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na II Takardar Sammace

April 5, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media