Shugaban kasar China Xi Jinping ya gayyaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da uwargidansa, Remi Tinubu, domin kai ziyarar aiki kasar Sin a watan Satumba.
Fadar shugaban ƙasa a jiya Juma’a ta tabbatar da hakan, inda hadiminsa Bayo Onanuga ya ƙara da cewa Tinubu ya amsa gayyatar wacce yake fatan za ta karfafa alakar Najeriya da kasar Sin da kuma yarjejeniyar musayar kudi da ake shirin yi.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da yan Najeriya ke cigaba da shirye-shiryen fita zanga-zanga a fadin kasar saboda yunwa da tsadar rayuwa












