Daga Hassan Umar Gwammaja
Gwamnan ya bayyana alhini da bakin ciki matuka kan kisan mutane 12 ‘yan asalin jihar a gundumar Mangun da ke karamar hukumar Mangu a Jihar Filato.
A cikin wata sanarwa da gwamnan ya sanya wa hannu da kansa wacce aka rabawa manema labarai a ranar Asabar, ya bukaci hukumomin tsaro da su tabbatar da kama wadanda suka aikata kisan tare da hukunta su yadda ya dace.
Gwamna Sani ya kuma roki gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, da ya dauki wannan lamari da muhimmanci. Ya ce: “Dole ne ya jagoranci ayyukan hukumomin tsaro domin ganin wadannan miyagu sun fuskanci hukunci.”
Tun da fari, Rundunar ‘yan sanda a Filato ta ce ta kama mutane 22 bisa zargin hannu a kisan baƙin biki 12 da aka kashe a kauyen Mangun, karamar hukumar Mangu.
Mai magana da yawun rundunar, Alfred Alabo, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar 21 ga Yuni, 2025.
Wadanda aka kashe na cikin motar haya mallakar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Kuma sun fito ne daga Zaria zuwa garin Qua’an Pan domin halartar biki.
Shaidu sun ce da misalin ƙarfe 8 na daren Juma’a ne mutanen suka tsaya don tambayar hanya, sai wasu matasa suka kai musu hari da muggan makamai, inda nan take suka kashe mutane 12, suka kona motar.












