Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana Musulunci a matsayin babban addini da ke koyar da ƙauna, zaman lafiya da kyawawan ɗabi’u.
Putin ya ce Musulmai mutane ne masu amana da kyawawan halaye, yana mai bayyana farin cikinsa da kasancewar al’ummar Musulmi masu yawa a ƙasar Rasha.
Shugaban na Rasha ya kuma yi Allah-wadai da masu alaƙanta Musulunci da ta’addanci, yana mai cewa babu wata alaƙa tsakanin addinin Musulunci da ayyukan ta’addanci.
Ya bayyana cewa ɗora laifin ta’addanci kan Musulunci zalunci ne, yana mai jaddada cewa za a ɗauki matakin hukunci mai tsanani a Rasha kan duk wanda ya yi ƙoƙarin danganta Musulunci da ta’addanci.
Putin ya ƙara jaddada muhimmancin mutunta addinai da kuma tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’ummomi daban-daban a ƙasar Rasha.










