Rahotanni sun ce manyan abokan hulɗar Rasha, musamman China da India, sun gargadi Shugaba Vladimir Putin da kakkausar murya kan yin amfani da makaman nukiliya. China ma ta sake bayyana cewa bai kamata Rasha ta yi tunanin amfani da makamin nukiliya a Ukraine ba.
A takaice, maganganun barazanar nukiliya suna karuwa, amma a halin yanzu babu wata hujja cewa Rasha tana shirya kai harin nukiliya a Ukraine.










