Shugaban ƙasar Burkina Faso, Captain Ibrahim Traoré, ya ƙaddamar da wata katafaren masana’antar ƙera tufafi a yankin Logofourousso, a birnin Ouagadougou, mai suna TEXFORCES-BF.
Masana’antar ta mamaye fili mai girman hekta 30. An bayyana cewa an kashe jimillar kuɗi da suka kai kusan Naira biliyan 17, idan aka canza kuɗin zuwa na Najeriya, wajen gina masana’antar, da suka haɗa da aikin gini, famfo da ruwa (plumbing), wutar lantarki, fenti, na’urorin aiki da sauran kayayyakin da ake buƙata.
A yayin ƙaddamar da masana’antar a ranar Laraba, 9 ga Satumba, 2026, Captain Ibrahim Traoré ya bayyana aniyar gwamnatinsa na ganin cewa audugar da za a yi amfani da ita wajen samar da tufafi a masana’antar ana nomanta ne a cikin Burkina Faso.
Ya ce ba wai za a noma audugar ne kawai a cikin ƙasar ba, har ma za a sarrafa ta a cikin gida kafin a mayar da ita kayan da za a yi amfani da su wajen ƙera tufafi.
A matsayin wani mataki na ƙarfafa gwiwar al’ummar ƙasar, tufafin sojoji ne daga cikin kayan farko da masana’antar ta fara samarwa. Shugaban ya kuma bayyana cewa ana sa ran masana’antar za ta samar da kayan sojoji da sauran kayan sawa na jami’an tsaron ƙasar gaba ɗaya.
Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin Burkina Faso na ƙarfafa masana’antunta da rage dogaro da shigo da kayayyakin da ake iya samarwa a cikin gida.









