Rahotanni daga jihar Zamfara sun ce wasu ’yan bindiga sun sace malaman addinin Musulunci shida bayan sun dawo daga gidan tsohon gwamnan jihar, Sanata Abdul’aziz Yari.
Bayanai sun nuna cewa malaman sun je gidan Sanata Yari da ke Talata Mafara ne domin halartar wani taron addu’a.
An ce malaman sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bakura da Talata Mafara, kuma ’yan bindigar sun tare su ne a kan hanyar da suke komawa gidajensu.
Har zuwa yanzu, ba a samu cikakken bayani kan halin da malaman suke ciki ko ko an tuntubi iyalansu kan batun ba.










