A yau, ina nuna goyon baya ga tsohon shugaban aikina kuma dattijon kasa, tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, yayin da yake tuna shekaru ashirin da rasuwar matar sa ƙaunatacciya, (Mrs) Stella Obasanjo.
Stella Obasanjo ba kawai uwa ce mai kulawa da mata mai biyayya ba, har ila yau mace ce mai halin kirki, basira da tausayi. A lokacin da take uwargidan ƙasa, ta yi aikin ne cikin natsuwa da cikakken jin kai, tana sadaukar da kanta wajen kula da yara, mata da marasa galihu. Gado da ta bari har yanzu yana haskaka hanyar hidima da jin ƙai ga al’umma.
“A wannan rana mai cike da alhini, ina mika jajircewata ga Shugaba Obasanjo da daukacin iyalan Obasanjo. Allah ya sa tunawarta ta kasance albarka, kuma Allah ya jiƙan ta ya ba ta hutu na har abada.”











