Daga: Hassan Umar Gwammaja
A lokacin ziyar, ya tunawa dukkan ma’aikatan Gwamnati dana Kananan Hukumomi nauyin da ke kansu,
da shawartasu su riki gaskiya, da rukon amana da kuma sadaukarwa wajen ba da kyakkyawar hidima ga jama’a.
Ya kuma yaba da jajircewar ma’aikatan Majalisar, Darakta Mai Kula da Majalisar, Rev. Daniel Nkrumah (wanda yanzu ya zama Babban Darakta), da Babban Jami’in Gudanarwa na Birni bisa jagoranci na musamman da kuma kyakkyawan aiki da suke yi don cigaban Birnin.
Majalisar Birnin Kwahu West na godiya ta musamman ga Majalisar Kula da Yankin Gabas bisa ci gaba da jagoranci, tallafi, da kwarin gwiwa da take bayarwa. Tare, muna ci gaba da himma wajen ba da ingantacciyar hidima mai inganci ga mutanen Kwahu West
A karshene Babba Jami’in Gudanarwa a Majalisar Koli Ta Gabas (Kwaho West) MC Hon. Tanimu Haliru ya yi godiya ga babban Jami’in akan wannan godinmawar da ya kawowa ma’ikanta, sannan ya yi fatan Allah ya mayar da su gida lafiya










