• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Gwamnan jahar Kano Abba Kabir Yusuf, Ya Yabawa Hukumomin Tsaron Jahar, Saboda Matakan Da Suka Dauka Akan ‘Yan Daba

aksam by aksam
April 12, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home TSARO
ADVERTISEMENT
481
SHARES
1.6k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA

Gwamnanan ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatin jahar, yayin gabatar da bikin Hawan Nasara a Ranar juma’a.

RelatedPosts

Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana neman jami’inta ruwa a jallo

Peace Corps of Nigeria Ta Yi Bikin Cika Shekaru 28 da Kafuwa

Jerin kamfanin tsaro na Amurka 10 da ‎China Ta Kakaba wa Takunkumi

A cewar gwamnan sun yi kokari wajen hada Kai da jami’an tsaro domin kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu, amma duk da haka sai da wasu marasa kishin jahar Kano, wadanda suka dawo da harkar Daba a cikin kwaryar birnin Kano.

Kano: Cikin Hotuna Yadda Wasu Matasa Suka Garkame Masallacin Juma’a Saboda Wani Dalili
Kotu ta ba da belin Emefiele kan naira miliyan 50
” Mun San su ba wai ba mu San su ba, sun dawo mana da Daba domin basa son cin gaban jahar Kano, kuma basa son zaman lafiya” Abba Kabir “.

Ya Kara da cewa a cikin watan Ramadan da ya gabata, an samu wasu batagarin matasa da suke rubuta wasika su aikata wa Mutane a masallatai, inda suke zuwa tare da farwa Mutane har su Yan yanke su ta Hanyar Daba mu su wukake, sannan kwace mu su wayoyinsu.

” Ba bu shakka gwamnatin Kano, a karkashin mu ba zata lamunci wannan ta’addanci da ake ba” Gwamnan Kano”.

Gwamnan jahar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya godiya wa shugabannin hukumomin tsaron jahar , da suka hada da Kwamishinan Yan sandan jahar CP Muhammed Usaini Gumel, Sojojin Kasa, Sojojin Sama, Hukumar tsaron Farin kaya DSS, hukumar gidan gyaran hali, hukumar kwastam da kuma ta shige da fice da dai sauransu.

Ya ce sun matukar kokarin domin dakile ta’addancin da aka shigo da shi , inda suka bi gida-gida wajen Kano dukkan Wanda aka ji labarin yana aikata ta’addanci , kuma aka gurfanar da su a gaban kotu.

Haka zalika gwamnan ya yi Kira ga mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, da su fito tare da hakimansa wajen bayar da gudunmawa don dakile wannan yanayi na ta’addanci.

” bayan an Kai su kotu mutane marasa kishin su suka je kotu, har suka bayar da kudi suka fito da wadanda aka Kama , a saboda haka gwamnatin Kano tana Allah wadai da wannan Abu, kuma su Masu yin hakan ko su Dakata su daina ko kuma gwamnati ta dira akansu” A.K.Y.”.

Ya Kara da cewa gwamnatin jahar Kano tare da hukumomin tsaro da Sarakuna za su Ci gaba da hada Kai, don tabbatar da cewar an ceto al’umma daga halin rashin tabbas da dardar.

” saboda haka mun dau matakai da za mu tabbatar da cewa wannan ta’addanci ya Kau cikin ikon Allah” Abba Kabir “.

Gwamnan ya ce a ko a watannin baya, da fadan Daba ya yi kamari a birnin Kano, sun janyo matasan 222 da suka tuba daga aikata laifuka har gwamnatin kanon, ta ba su sana’o’in dogaro da Kai.

Da yake nasa jawabin mai martaba sarkin Kano, Alhaji Dr. Aminu Ado Bayero, ya bukaci gwamnatin jahar, ta Kara Himma wajen gyaran tarbiyar matasa da kuma yin aiyukan sa za su kawo ci gaban Kano.

Share192Tweet120SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Innalilahi Wa’inna ilahi Rajiun !!!

Next Post

GAYYATAR DAUREN AURE !!!

aksam

aksam

RelatedPosts

Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana neman jami’inta ruwa a jallo
TSARO

Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana neman jami’inta ruwa a jallo

by Khadija Maitaya
July 24, 2026
Peace Corps of Nigeria Ta Yi Bikin Cika Shekaru 28 da Kafuwa
LABARAI

Peace Corps of Nigeria Ta Yi Bikin Cika Shekaru 28 da Kafuwa

by Khadija Maitaya
July 10, 2026
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka
LABARAI

Jerin kamfanin tsaro na Amurka 10 da ‎China Ta Kakaba wa Takunkumi

by Khadija Maitaya
June 22, 2026
Rundunar  Sojin Najeriya Ta Yi Nasarar Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Abubakar Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane
TSARO

Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Nasarar Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Abubakar Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

by aksam
June 16, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

De Toegankelijkheid van Online Casinospellen op Mobiele Apparaten: Een Diepgaande Analyse

April 21, 2025
Labaran yamma tareda khadija Muhammad maitaya

Labaran yamma tareda khadija Muhammad maitaya

November 6, 2023
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media