• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Aron kalma a yaren Hausa da yadda Bahaushe ke bi wajen aro kalmomi a wasu yarukan

aksam by aksam
October 27, 2023
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
469
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

ARON KALMA (WORD BORROWING)

A da can kafin zuwan addinin Musulunci da Turawan Mulkin Mallaka Hausa mutane da suke da fasaha, da tsarin rayuwa bisa tada (al’ada) ta yanki daban-daban. Hausawa suna magana da harshensu na Hausa. Hausa kuwa ta kasance ta yanki-yanki, kowanne yanki na da irin karin harshe da zaɓar kalmomi da yake amfani da su wajen furta magana da isar da sakwanni

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Da yake Hausawa na da yalwar kalomomi, ga fasaha wajen sarrafa kalma (syntax/الصرف) da zaɓar  kalmomi, da kuma amfani da su, duk da haka bai hana Hausawa amfani da kalmomin aro ba saboda baƙin abubuwa da suke shigowa cikin Hausawa wandanda ada can basu da shi; misali: mota, bindiga, kwalfuta, tarho da sauran su

Kuma yawanci wadanda suke shigowa da Hausawa baƙin abubuwa da farkon-farko Addinin Musuluncine (Larabci), Labarawa ƴan kasuwa da Turawan Mulkin Mallaka (Ingilishi), sai kuma wanda Hausa ke cuɗayya da su wajen zama kamar Fulani, Yarbawa, Kanuri, Swahili da sauransu. Hausawa na aro kalmomin Larabci da Turanci da ma sauran yarunka da Hausawa ke cuɗanya da su ta hanyoyi biyu; ‘Loanword’ (aron kalma da amfani da ita kai tsaye); da kuma ‘Loan Blend’ (aron kalma tare da ‘dan yi mata kwaskwarima)

Ta ɓangaren aron kalma kai-tsaye (Loanword); Hausawa na aro bakin kalmomi daga wasu yaruka (e.g. Larabci (Arabic) da Ingilishi (English) da sauransu) mafiyawanci hanyoyi uku (3) Loanword, ɗaya (1) Loan blend, in aka haɗe huɗu (4) kenan:

HANYA TA FARKO:
Hausa kan aro kalmar Larabci ko Ingilishi saboda zuwa da baƙin abubuwan da ada Hausawa basu da shi na ƙirƙira (fasaha/technology), ilimi, tsarin mulki, cuɗayya (muamala}, misali:

Bindiga (البندقية), waya (wire), hankacif (handkerchief), alkalami (القلم), biro (biro), tarho (telephone), taya (tyre/tire), bukiti (bucket), jami’a (الجامعة), kwaleji (college) sukari (sugar/السكر), kwalfuta (computer), lantarki (electrical), akawu (accountant), kwala (collar), fanka (fan), gwamna (governor), biskit (biscuit), hijabi dss.

HANYA TA BIYU:
Hausawa su kan aron kalma Larabci ko Ingilishi sai su musanya wadanda suka aro da nasu na tuntuntuni (na asali), misali:

Sani = ilimi (العلم), wadata = arziki (الرزق), kwartanci = zina (الزنا), rashin sani = jahilci (الجهل), daidai = adalci (العدل), madubi = miro (mirrow), likidiri = bukiti (bucket), laulawa = keke (daga larabci), kaico = nadama (الندم), magana = kalami (الكلام), raga = net, karkarwa = babreshin (vibration), lambu = gadina (garden), magatakarda = sakatare (secretary), da sauransu.

HANYA TA UKU
Hausawa su kan aro kalmomin wasu yaruka gudabiyu (2) ko fiye, sai su hadesu a waje guda (hybrid) su kuma yi amfani da su, su yi magana da junansu, su kuma fahimta, misali:
Kofin-shayi (kofi = cup (English), shayi =الشي (Arabic)); injin biredi (inji = engine (English from Latin ‘ingenium’), biredi/borodi = bread (English)), alkalin kotu (alkali = القاضي (Arabic), kotu = court (English)), da sauransu.

HANYA TA HUDU (LOAD BLEND)
Hausa kan aro kalma daga wani yare, sai cakuɗata da ta su ta asali (load blend) ta kuma bada cikekkekiya ma’ana, misali:
Maficin roba (mafici = abin fifitawa/bada iska (Hausa), roba = rubber (English)); injin nika (inji = engine (English), nika = mirzewa/faffasa abu zuwa kananu (Hausa)),
Makaranta = (ma = ɗafi {affixation, prefix} na karin ma’ana da ke nuna wajen aiki e.g. ma’aikata (inda ake wani aiki), majema (inda ake jime fatu), manoma (inda ake noma) dss (Hausa), karanta = daga karatu, karatu daga قرأت ie. na yi karatu (Arabic)).

Manazarta: Aliyu M. Ahmad blog sport. Con

Tags: AmsoshiBbchausaDailyTrusteducationguardian newspaperLegit.ngpremium timespsychologypunch Newspaperrfi hausaSolacebaseVanguard newspapervoahausa
Share188Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Hanyoyin sadarwa na gargajiyar Bahaushe

Next Post

Dalilan kamfanin KEDCO na dauke wutar lantarki na tsawon awa 12 a gobe Lahadi

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Moon Sighting, Sultan gives order to look for crescent today Monday 8/4/2024

April 8, 2024

Bezpieczeństwo i poziom rozgrywek w kasynach online – analiza i wyzwania

April 21, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media