Daga: Hassan Umar Gwammaja
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya aiyana dokar ta baci a jihar Rivers.
Idan za a iya tunawaAksam media ta rawaito ana ta rikicin Shugabanci a jihar Rivers, yayin da ake samu rashin jituwa tsakanin gwamnatin jihar da bangaren majalisar dokokin jihar.
Shugaban kasar ya aiyana dokar ne bayan wata ganawa da ya yi da shugabannin hukumomin tsaron kasar kan rikicin jihar ta Rivers.
Yanzu haka dai za a iya cewa ba gwamnati a jihar har sai matakin da shugaban kasar ya dauka .
Rahotannin sun tabbatar da cewa shugaban kasar ya dakatar da gwamnatin jihar da dukkanin ‘yan majalisar dokokin jihar har na tsahon watanni shida.










