Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza.
Rahotanni sun ce an sace Mai Shari’ar ne da sanyin safiyar ranar Lahadi a gidansa da ke kan titin Zogirma a ƙaramar hukumar Bunza ta Jihar Kebbi.
Majiyoyi da suka zanta da SolaceBase sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na dare, jim kaɗan bayan Mai Shari’ar ya dawo daga tafiya zuwa Jihar Sokoto.
Wata majiya ta ce, “Ya dawo ne daga Sokoto, sai wasu ɗauke da makamai da ake zargin ‘yan bindiga ne suka mamaye gidansa suka yi awon gaba da shi.”
Majiyar ta ƙara da cewa, babu wani daga cikin mutanen gidan da ya samu rauni, sai dai maharan sun riƙa harbe-harbe a iska kafin su tafi da Mai Shari’ar zuwa inda ba a sani ba.









