DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
EFCC, ta gurfanar da Aisha Malkohi da Sani da Ummitah, (Arab Money) da mijinta, mai suna Abubakar Mahmoud, bisa zargin laifin damfarar Naira miliyan 410.5.
A gaban wata babbar kotun jihar Kano, ya yin da mijinta ya arce, a cewar wata sanarwa da EFCC ta fitar ranar Litini dinnan.
Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana a cikin sanarwar cewa wanda ake tuhuma an gurfanar da ita a gaban kotu bisa zargin tuhume-tuhume biyar da suka shafi damfara na kudade har N410,518,000.
Hukumar tace wadda ake zargin a jihar Kano, biyo bayan karar da wasu masu shigar da kara guda biyu Farida Ibrahim da kuma Ibrahim Mohammed Abdulrahman, suka shigar, inda suke zargin ta hada baki da mijinta suka damfare su.
Masu ƙara sun ce ta damfare su ta hanyar amshe musu kuɗi da sunan za ta siyo musu motoci 64, gwalagwalai, da kayan wuta daga Saudiyya.
Bayan haka ne sai hukumar ta tsunduma farautar su da kuma bin diddigin abinda ya faru. EFCC ta gano cewa an jibga naira miliyan 410 a asusun wani kamfani mai suna Golden Grass, wanda mallakin wannan mata ce da mijinta.
Sannan an gano sun rika canja wa kuɗaɗen asusun ajiya ta hanyar rarraba su ita da mijinta zuwa wasu asusun ajiyan.












