Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin ƙarfafa ayyukan tsaro da yaƙi da ’yan bindiga a faɗin Jihar Kano, musamman a yankunan Garun Mallam, Beli, Bebeji da kuma Gwarzo.
Matakan sun haɗa da ƙara jami’an tsaro, inganta tattara bayanan sirri, gudanar da ayyukan sintiri na haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da ’yan sa-kai, tare da ƙarfafa haɗin gwiwar al’umma wajen bayar da sahihan bayanai domin hana hare-hare da kare rayuka da dukiyoyi.
Manufar matakan ita ce ƙarfafa zaman lafiya da tsaro ga al’ummar jihar Kano, tare da tabbatar da cewa hukumomin tsaro suna mayar da martani cikin gaggawa domin dakile barazanar tsaro.









