31/08/26
By Khadija Muhammad Maitaya
A kokarin Gwamnatin Jihar Kano na yaki da harkar daba da kwacen waya,hakan yasa ta kafa Majalisar Matasan da ke da alaka da harkar daba, domin samar da hanyoyin sasanta rikice-rikice da kawo ƙarshen fadan daba a jihar.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya kafa majalisar, wadda za ta samar da wata kafa ta tattaunawa da fahimtar juna tsakanin matasan da abin ya shafa.
Majalisar, ƙarƙashin jagorancin Malam Abdullahi, za ta yi aiki tare da wasu kwamitoci da aka kafa domin gano musabbabin fadan daba da kuma samar da hanyoyin magance matsalar tun daga tushe.
Kwamitocin za su mayar da hankali wajen sasanta rikice-rikice tsakanin ƙungiyoyin matasa, da wayar da kan matasa kan illolin daba, tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
Kwamishina Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce gwamnatin Kano ta himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro, musamman ganin yadda matsalar daba ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a wasu sassan jihar.
Ya kuma yi kira ga matasa da su rungumi zaman lafiya, yana mai cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, matasa da al’umma shi ne hanya mafi dacewa wajen kawo ƙarshen matsalar daba a Kano.









