Hukumar DSS ta kama wani mutum mai suna Moferewa Maiye da ake zarginsa da yin sojan gona a babban birnin tarayya Abuja
An kama jami’in Bogin ne sanye da kayan aiki irin na jami’an DSS tare da bindigar bogi, bayan an zarge shi da tsoratar da masu abubuwan hawa
Jami’an tsaro sun bi sawun mutumin har zuwa maboyarsa da ke kusa da kwanar NITEL da ke Wuse II, Abuja, inda suka cafke shi tare da kayan aikin da yake barazana da su ga al’umma.
Jami’ai na gudanar da bincike domin gano tsawon lokacin da wanda ake zargin ya dauka ya na gudanar da irin wadannan ayyukan na yin sojan gona na amfani da Kayan jami’an tsaro domin karbar na goro
A yayin da ake yi masa tambayoyi, Maiye ya ce ya fito ne daga kauyen Agbajojun da ke karamar hukumar Mopamuro ta jihar Kogi.










