Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta musanta rahotannin da ke cewa shugabanta, Farfesa Joash Amupitan, ya taba amfani da wani asusun kansa a dandalin sada zumunta na X, wanda a kira Twitter wajen nuna goyon bayan jam’iyyar APC.
Wannan martani ya biyo bayan yaduwar wani sako a kafafen sada zumunta da ake dangantawa da shi, inda aka yi zargin cewa ya bayyana cewa “nasara tabbatacciya ce” ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki gabanin babban zaben shekarar 2023.
Wani sako da ya karade kafafen sada zumunta, wanda aka wallafa a ranar 18 ga Maris, 2023, ya kasance martani ne ga wani sako da shugaban matasan APC na kasa, Dayo Israel, ya wallafa. A cikin sakon nasa, Israel ya yi ikirarin cewa ya taimaka wajen karkatar da kuri’u zuwa ga APC a wata al’umma da galibin mazaunanta ‘yan kabilar Igbo ne a jihar Legas.
Sai dai INEC ta bayyana cewa duk wani sako da ake yadawa da sunan shugabanta a dandalin X ba gaskiya ba ne, tare da jaddada cewa ba shi da wani asusun kansa a wannan dandali.










