Adnan Oktar Malamin Addinin Islama Ne a Kasar Turkiyya Wanda Aka Yankewa Daurin Shekaru 8,658 Saboda Laifin aikata Badala
A ranar 17 ga Nuwamba, 2022, an yanke masa hukuncin daurin shekaru 8,658 a gidan yari saboda ya jagorantar gungun masu aikata laifukan badala, yin leken asiri na siyasa da na soja, lalata da kananan yara, da sauran tuhume-tuhume.
Wata kotu a birnin Istanbul ta yanke hukuncin daurin shekaru 8,658 a gidan kaso ga wani ma’aikacin gidan talabijin da ya kewaye kansa da wasu mata masu sanye da kayan kwalliya da ya kira ‘ya’yan kyanwa.
Adnan Oktar, wanda aka bayyana a matsayin “shugaban kungiyar asiri”, ya jagoranci shirye-shiryen talabijin da mata ke kewaye da shi yayin da yake wa’azin halitta da dabi’un mazan jiya.
Ya kuma buga littafai cikin harsuna da dama a duniya, karkashin sunan alkalamin Harun Yahya.
An kama Adnan Oktar mai shekaru 66 da daruruwan mabiyansa a shekarar 2018 bayan wani samame da ‘yan sanda suka kai a Villa dinsa, ya nuna cewa yana gudanar da wata kungiyar masu aikata laifuka a karkashin wata kungiyar asiri ta addinin Islama wadda ta yi kamfen na kin jinin juyin juya hali na kasa da kasa, da gidajen buga littattafai da kafafen yada labarai daban-daban.
An kuma rufe tasharsa ta A9 TV ta yanar gizo.












