Daga Hassan Umar Gwammaja
Ya karbi gaisuwa ne a Filin Sauka da Tashin Jiragan Sama Na Tunawa Da Malam Aminu Kano,
Tunanin jama’a ya mayar da hankali ne kan wannan ganawa, ganin cewa tun bayan rikicin da ya biyo bayan sauya tsarin masarautun Kano, ba a hangi Sardaunan Kano yana gaisawa ko mubayi’a da kowanne bangare na sarautar ba.
Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Dakta Ado Bayero, ne ya naɗa Malam Ibrahim Shekarau a matsayin Sardaunan Kano
Bayan Khalifa Muhammad Sanusi II ya hau gadon sarauta a shekarar 2014, bai sauke Shekarau daga mukaminsa ba, ya kuma ci gaba da aiki da shi har zuwa lokacin da gwamnatin tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta tube Sanusi daga sarauta a shekarar 2020.
Wannan ganawa da karɓar gaisuwar da aka gani yanzu tsakanin Sarkin da Sardauna, na iya zama wani muhimmin al’amari a tarihin masarautar, duba da matsayin da Shekarau ke da shi a masarautar da kuma siyasar Kano da kasa baki ɗaya.











