• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kasar Turkiyya ta gana da Burkina faso domin inganta tsaro

aksam by aksam
May 19, 2025
Reading Time: 1 min read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Burhanettin Duran, ya kai ziyara a hukumance zuwa Burkina Faso a ranakun 13-14 ga watan Mayu domin karfafa dangantakar kasashen biyu da tattauna batutuwan tsaro, kamar yadda majiyoyin Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya suka bayyana.

A yayin ganawarsa a Burkina Faso, Duran ya tattauna kan ci gaban da ake samu a yankin Sahel da Burkina Faso, musamman ma kan yaki da ta’addanci, tare da tattauna dangantakar kasashen biyu da sauran fannoni na hadin gwiwa.

RelatedPosts

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano

A lokacin ziyarar, Duran ya samu tarba daga Firaimistan Burkina Faso, Jean Emmanuel Ouedraogo, sannan ya tattauna da Ministan Harkokin Waje, Karamoko Jean Marie Traore.

Firaminista Ouedraogo ya jaddada cewa akwai karfin gwiwa daga bangarorin biyu wajen fadadawa da ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Minista Traore ya bayyana cewa Turkiyya abokiya ce mai aminci a lokuta da ake cikin mawuyacin hali, inda ya ce tana bayar da taimako ga Burkina Faso a lokacin da take fuskantar ƙalubale na ta’addanci, kuma Turkiyya ta taka rawa wurin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Burkina Faso da kuma kawar da ta’addanci daga kasar.

Traore ya kara da cewa suna kallon Turkiyya a matsayin kyakkyawar abokiyar hulɗa, kuma suna da niyyar ƙara ƙoƙari wajen ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Ouagadougou da Ankara.

A lokacin ziyarar, an rattaba hannu kan yarjejeniyoyi guda biyu tsakanin ma’aikatun harkokin wajen kasashen biyu.

An amince da cewa za a tattauna kan shawarwarin siyasa da za su kunshi dukkan fannoni na dangantakar kasashen biyu a Ankara cikin wannan shekara.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Shugaba Bola Ahmad Tinubu Ya Gana Da Peter Obi, Fayemi A Fadar Vatican

Next Post

Gwamnan Borno ya roki gwamnatin tarayya Abu ɗaya domin yanta Garin Marte daga yan Boko Haram

aksam

aksam

RelatedPosts

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi  Annabi Muhammadu SWA  A Garin Nkawkawo
Uncategorized

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

by aksam
September 1, 2026
Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka
Uncategorized

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

by aksam
August 26, 2026
Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano
Uncategorized

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano

by aksam
August 26, 2026
Gwajin DNA: Kashi 23.6% Na Gwaje-Gwajen Uba A Najeriya Sun Nuna Rashin Daidaito
Uncategorized

Gwajin DNA: Kashi 23.6% Na Gwaje-Gwajen Uba A Najeriya Sun Nuna Rashin Daidaito

by aksam
August 25, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Rudunar  ‘Yansandan Jihar Adamawa Ta Cafke Wani Matashin Da Ake Zargin Da Hallaka Jami’in Kotu Bayan Ya Kai  Masa Takardar Sammaci

Rudunar ‘Yansandan Jihar Adamawa Ta Cafke Wani Matashin Da Ake Zargin Da Hallaka Jami’in Kotu Bayan Ya Kai Masa Takardar Sammaci

December 20, 2023
Yadda wani gwamna ya yi koyi da Gwamnan jinar kano Abba Kabir Yusuf

Yadda wani gwamna ya yi koyi da Gwamnan jinar kano Abba Kabir Yusuf

January 29, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

August 23, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media