• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Cikakken rahoto kan batun zuwa sojojin Faransa Najeriya.

aksam by aksam
December 16, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
468
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga ƙarshen makon da ya gabata zuwa farkon wannan mako, an riƙa yaɗa wani faifan bidiyo a kasar nan cikin harshen Hausa, wanda a ciki ake iya ganin wani jami’in sojin Najeriya tare da wani soja farar fata a bayansa.

Masu yaɗa bidiyon sun bayyana cewa baturen da ke cikin bidiyon ɗaya ne daga cikin sojojin Faransa da suka isa jihar Borno da ke Najeriya domin taimaka wa sojin Najeriya wajen yaƙi da mayaƙan Boko Haram.

RelatedPosts

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Borno jiha ce da ta kasance cibiyar rikicin Boko Haram, ƙungiya da ta shafe sama da shekara 10 tana kai hare-hare kan jami’an tsaro da farar hula a yankin arewa maso Gabas na kasar nan .

Rikicin wanda ya shafi ƙasashe masu maƙwaftaka, kamar Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru ya yi sanadin rasa rayukan mutum aƙalla 36,000 da kuma tarwatsa wasu mutanen fiye da miliyan ɗaya.

Duk da cewa sojojin Najeriya sun samu nasarar rage kaifin hare-haren ƙungiyar, har ma a baya hukumomi suka ayyana ‘yin galaba’ a kanta, har yanzu mayaƙan ƙungiyar na kai hare-hare lokaci zuwa lokaci.

Ba dai sabon abu ba ne a ga ƙasashen da ke fama da irin waɗannan rikice-rikice na samun taimakon ƙasashen duniya a ƙoƙarin daƙile irin waɗannan ayyuka na masu ƙungiyoyin masu tayar da tarzoma.

Shi ya sanya kafin yanzu, wasu daga cikin ƙasashen yammacin Afirka da na Sahel suka bai wa manyan ƙasashen duniya damar kafa sansanonin soji a cikinsu da sunan yaƙi da ayyukan ta’addanci a yankin.

Sai dai bayan juyin mulki a Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkin Faso, ƙasashen uku sun raba gari da uwargijiyarsu Faransa da kuma Amurka da ma wasu ƙasashen Turai, ta hanyar katse yarjejeniyoyi na tsaro da su.

To amma mece ce gaskiyar bidiyon da ake yaɗawa na cewa sojojin Faransa sun isa Najeriya a wani yunƙuri na kafa sansani?

A tattaunawarsa da manema labarai, daraktan yaɗa labarai na shalkwatar tsaro ta Najeriya, Birgediya-Janar Tukur Gusau ya musanta batun isar tawagar sojin Faransa Najeriya.

Ya ce “idan za a iya tunawa, tun kafin ma a saki wannan bidiyo, CDS (Babban hafsan sojin Najeriya) ya faɗi cewa babu wata yarjejeniya domin kawo sojojin Faranshi a kowane yanki na faɗin Najeriya”.

Janar Gusau ya bayyana cewa bidiyon da ake yaɗawa tsoho ne kuma ba sojojin Faransa ba ne a cikin bidiyon.

Tun farko, shalkwatar tsaro ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa da safiyar ranar Litinin tana musanta kasancewar sojin na Faransa a Najeriya.

Sanarwar, wadda ta samu sa hannu daraktan kula da sashen yaɗa labaru na shalkwatar tsaron, Manjo-Janar Edward Buba, ta ce “an janyo hankalinta kan wasu rahotanni da ake yaɗawa a shafukan intanet da ke cewa wata tawagar sojin Faransa ta isa Maiduguri a wani yunƙuri na kafa sansanin sojin Faransa a arewa maso yammacin Najeriya”.

“Wannan bayani ƙage ne, ƙarya ce kuma an yi ne da wata manufa,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Bayan sauke wasu mukarraban sa, Gwamnan Kano ya nada manyan Malamai 46 a majalisar Shura.

Next Post

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da nada shugabannin raya kogunan da suke karkashin ma’aikatar Ruwa ta tarayyar Nigeria.

aksam

aksam

RelatedPosts

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala
LABARAI

Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala

by aksam
April 17, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID
Uncategorized

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

by aksam
April 17, 2026
Araqchi Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matsaya Ka
Uncategorized

Araqchi Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matsaya Ka

by aksam
April 11, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Kungiyar masu safarar shanu tayi wani albishir ga Iyalan yankungiyar da suka rasu

Kungiyar masu safarar shanu tayi wani albishir ga Iyalan yankungiyar da suka rasu

April 9, 2024

China na kausasa martani kan kasar Amurka

January 14, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media