Daga: Maryam Muhammad Suleiman
Kimanin ƴan bindiga 37 ne aka kashe a garin Matusgi da ke karamar hukumar Ƙaura Namoda a jihar Zamfara, bayan da mazauna kauyen Matusgi suka fuskanci wasu ‘yan bindiga da suka mamaye garin da nufin yin garkuwa da mutane.
A cewar wani mazaunin garin da ba’a bayyana sunansa ba, ‘yan bindigar sun zo ne akan babura da karfe biyu na rana, a ranar Larabar da ta gabata, da nufin yin garkuwa da mutane, yana mai cewa ba shi ne karon farko da alummar garin suka fuskanci ‘yan bindiga ba, amma karon farko ne da suka yi nasara akan yan bindigar.
Mazaunin garin ya ce ‘yan bindigar sun fara kai harin ne ta hanyar harbi da bindiga domin tsoratar da al’umma, sai dai duk da haka mutanen garin basu ja da baya ba.
Ya ce wasu mutanen garin dauke da bindigogin mafarauta sun yi artabu da su, yayin da wasu kuma suka yi amfani da makaman wajen kewaye yankin, tare da hana ‘yan fashin tserewa.
Bayan an dauki tsawon sa’a guda ana gwabza kazamin fada, ‘yan bindigar sun ja da baya, inda aka ce mambobinsu 10 sun mutu.
Daga nan sai mazauna garin suka sake haduwa suka yi kwanton bauna, a lokacin da ‘yan fashin suka dawo, mutanen garin sun sake kai hari, inda suka kashe ‘yan bindiga 37 baki daya.
Hakimin Matusgi, Alhaji Ciroma Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kashe mutanen garin uku a rikicin.
Ya kara da cewa, kauyukan da ke makwabtaka da su sun ba da rahoton ganin ‘yan bindigar na jigilar gawarwakin ‘yan uwansu da suka mutu.












