Daga Hassan Umar Gwammaja
Wata majiya ta rawaito shugaban ya kuma amince da dakatar da biyan riba da aka samu a 2024 ga gwamnati don taimakawa da kuɗaɗen da kamfanin zai kashe.
Ko da yake Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, sai dai akwai alamun da ke nuna cewar har yanzu gwamnati na kashe kuɗaɗe masu yawa a kan tallafin.
Idan ba a manta ba, ‘yan Najeriya sun yi zanga-zanga saboda wahalar da ake ciki a ƙasar, kuma ɗaya daga cikin buƙatunsu shi ne a dawo da tallafin man fetur.
Amma a cikin wani jawabin da Tinubu ya yi, ya bayyana cewa dawo da tallafin man fetur ba zai yiwu ba, inda ya bayyana cire tallafin a matsayin abu mai wahala amma kuma wajibi ne gwamnatinsa ta yi.
Ya ce tallafin ya kasance tamkar wata sarƙa da ta ɗaure tattalin arziƙin Najeriya.
A ranar Litinin, wata jarida a Intanet ta ruwaito cewa Tinubu ya amince wa NNPCL da ya biya tallafin bayan da kamfanin ya koka cewa ya yi amfani da duk hanyoyin da zai iya don samar da isasshen man fetur a ƙasar nan amma hakan ya gagara.
NNPCL ya shaida wa shugaban cewa waɗannan ƙoƙarin sun gaza warware matsalar da ake fuskanta, kuma idan ba a biya tallafin ba, kamfanin ba zai iya sanya kuɗin da ake buƙata daga gare shi ga asusun Gwamnatin Tarayya ba.
Don haka, Tinubu ya umarci kamfanin da ya yi amfani da haraji da sauran kuɗaɗen da aka ware wa Gwamnatin Tarayya domin biyan kuɗaɗen tallafin man fetur.











