Daga Maryam Muhammad Suleiman
A wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, shugaban jam’iyyar APC, Alhaji Abdullahi Abbas, ya bukaci a rufe asusun kananan hukumomin jihar domin a daina ci gaba da kwashe dukiyar al’umma da sunan ayyukan hadin gwiwa.
Ya ce amincewar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi na cewa bai san da wannan badakalar ba, wata alama ce da ke nuna cewa ko dai ba shi da iko akan gwamnatin ko kuma rashin iya shugabancin jihar kamar yadda APC take zargi .
Abbas ya bayyana cewa umarnin da gwamna ya baiwa hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano abun dariya ne.
Shugaban jam’iyyar ya yi nuni da cewa, shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ya na da bangaranci, kuma ba shi da hurumin bincike kan badakalar da ake zargin yan uwan uban gidan gwamnan kuma jagoran NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Abdullahi Abbas ya kara da cewa gwamnatin jihar ta bayar da kwangilar aikin gada akan kudi Naira biliyan 27, inda za a gina gada guda biyu a mahadar Dan-Agundi da Tal’udu a cikin babban birni, wanda za a dauko kashi 70 cikin dari na kudaden Kananan hukumomi 44.












