Daga Hassan Umar Gwammaja
Kungiyar masu gidajen burodi ta kasa reshen jihar Kano ta koka kan yadda ta samu karin Naira dubu 20 a duk buhu daya na fulawa a kasuwar Singa.
Shugaban kungiyar a Kano, Jibrin Abubakar Hamza, ya ce kafin fara zanga-zanga, suna sayen buhun fulawa daya a kan Naira dubu 65. Amma daga shekaran jiya zuwa yau, Alhamis, da aka bude kasuwar Singa, farashinta ya yi tashin gwauran zabi inda ya kai dubu 85 a duk buhu daya.
Abubakar ya ce sun tuntubi kamfanin fulawa inda aka tabbatar masu da cewa buhun fulawa yana nan kan Naira dubu 60 da 450.
Jibrin Abubakar, ya ce tsadar ta sa su yanke shawarar rufe gidajen burodi a fadin Kano da zarar fulawa mai sauki da suke da ita ta kare.
Kungiyar masu gidajen burodi ta bukaci mahukunta su shiga cikin lamarin domin al’umma su samu saukin rayuwa.
Aksam Media, ta ruwaito cewa ko a ranar Laraba, shugaban kasuwar Singa, Musa Ibrahim Na Banki, ya ce ba za su lamunci yan kasuwa marasa tsoron Allah su zuba ido suna cin karensu babu babbaka ba game da tashin farashin kayayyaki a kasuwa, inda ya ci alwashin cewa za su taka masu burki.












