Majalisar Dokokin Jamus wato Bundestag ta amince da wata sabuwar doka da ta sassauta matakan bai wa baki ‘yan kasashen ketare zama ‘yan kasa.
Dokar ta rage shekarun mallakar fasfon daga takwas zuwa biyar.
Bayan an Jima ana kai ruwa rana a ranar Juma’ar da ta gabata, Majalisar Dokokin Jamus ta amince da bai wa wadanda suka shafe shekaru biyar a kasar fasfo na dan kasa, idan suka cika wasu ka’idojin a maimakon shekaru takwas zuwa goma.
Sanarwar dai ta jefa dubban mutane cikin yanayi na farin ciki, musamman wasu ‘yan kasashen Afirka da ke rayuwa a kasar.
To kashi goma sha takwas cikin dari na al’ummar Jamus dai baki ne kamar yadda kididdiga a kasar ta nunar, da dama daga cikin su sun shafe shekaru ba tare da sun sami takardar ba, saboda tsaurin matakan samun takardar.
Yanzu dai sabuwar dokar ta amince mutum ya ci gaba da amfani da fasfo na kasarsa ta asali, sabanın yadda a baya dokar ta Jamus ba ta yadda da hakan ba, idan har mutum bai fito daga Tarayyar Turai ba, amma kuma akwai kasashe kamar Ghana da Kamaru da dokar kasarsu ba ta amince musu zama ‘yan wata kasa baya ga kasar a lokaci guda ba.
Leo King dan Kamaru ya ce ‘’Duk da na ji dadin wannan labarin amma sai murna ta koma ciki gani na a matsayina na dan Kamaru kafin na ci gajiyar dokar sai na sallama fasfona na Kamaru, wanda hakan ya saka ni cikin bakin ciki, amma fatana naga gwamnatin Kamaru ta sake nazari ta sassauta matakinta don muma mu ci gajiyar tsarin na amfani da fasfon kasashen biyu tare.”
Bugu da kari dai, sabuwar dokar ta tanadi a bai wa wadanda suka cika shekaru uku a kasar katin dan kasa na dindirdin, musanman ga wadanda suka ba da himma a lakantar harshen Jamusanci da kuma sajewa da al’adun kasar.












