Tsofaffin kwamishinoni takwas na Kaduna sun yi karin haske kan rahoton majalisar jihar da ya zargi tsohuwar gwamnati da almundahana
Tsofaffin mukarraban gwamnatin sun karyata rahoton majalisar da ya ce gwamnatin El-Rufai ta karkatar da Naira biliyan 423
Hakazalika tsofaffin kwamishinonin sun ce akwai basussukan da gwamnatin El-Rufai ta nemo amma gwamnatin Uba Sani ce ta karbi kudin
A zantawarsu da manema labarai a Abuja, a ranar Talata, tsofaffin kwamishinoni takwas na gwamnatin El-Rufai sun karyata zarge-zargen majalisar Kaduna, inji rahoton Leadership.
Tsofaffin jami’an sun yi watsi da zargin da ake yi wa gwamnatin El-Rufai na cewa ita ce ta karbo dukkanin basussukan da suka yi wa jihar katutu a yanzukafin ta bar ofis a Mayun 2023.
Sun kuma bayyana zargin da majalisar dokokin Kaduna ta yi na cewa tsohuwar gwamnatin ta karkatar da kudaden jihar N423bn a matsayin rashin adalci.
Tsofaffin kwamishinonin da suka yi magana da manema labarai sun hada da Jafaru Sani (ma’aikatar muhalli da ilimi), Hafsat Baba (ma’aikatar jin dadi da bunkasa jama’a) da Thomas Gyang (ma’aikatar ayyukan, da tsare-tsare da kasafin kudi).
Sauran sun hada da: Bashir Saidu (ma’aikatar kudi); Ibrahim Husaini (ma’aikatar noma da muhalli), Aisha Dikko (ma’aikatar shari’a), Fausat Ibikunle (ma’aikatar gidaje da raya birane), da Idris Nyam (ma’aikatar kasuwanci, da kirkira da fasaha).
Sun bayyana tuhumar da majalisar ta yi a matsayin kamfe na batanci ga tsohon gwamnan, inda suka bayyana cewa rahoton ya dogara ne da wasu alkaluma da aka gina su akan karya.












