Daga Hassan Umar Gwammaja
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai, yace marigayin ya rasu a yau Laraba a kasar Misira
Ya ce Gwamna Yusuf, wanda ya nuna kaɗuwa ga rasuwar Bunkure, ya baiyana mutuwar ta sa matsayin babban rashi ga iyalinsa da ma Kano baki ɗaya.
“Wannan wani yanayi ne na kaɗuwa da alhini saboda Injiniya Bunkure mutum ne mai hazaƙa da sanin makamar aiki wanda jihar Kano za ta amfani da shi.
” Allah Ya gafarta masa Ya baiwa iyalin sa da mu baki ɗaya hakurin rashin sa,” in ji Gwamnan.












