• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Cikakken rahoto akan binciken da ake yiwa tsohon shugaban CBN

aksam by aksam
December 24, 2023
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
469
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

SAUYA LAUNIN NAIRA: ‘Yadda Sabi’u Tunde Ya Ba Emefiele Shawarar A Sauya Wa Naira Launi, Cewar Mai Binciken Musamman

A ci gaba da bankaɗo harƙallar gagarimar sata da gadangarƙamar karkatar da maƙudan biliyoyin kuɗaɗen Najeriya da ake zargin tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya tafka, Mai Binciken Harƙalla na Musamman ya damƙa wa Shugaba Bola Tinubu rahoton abin da ya bankaɗo a CBN, wanda Majiyar Focus News Hausa PREMIUM TIMES Hausa ta fara bugawa daki-daki.

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

Cikin rahoton, Mai Bincike Obazee ya bayyana cewa tun asali CBN ya aika wa Kwamitin Gwamnonin CBN shawarar za a sauya launin kuɗi.

Babban Daraktan Hada-hadar Kuɗaɗe na lokacin, Ahmed Umar wanda ke ƙarƙashin Mista Folashodun ne aka sa ya rubuta masu wasiƙar a ranar 25 ga Agusta, 2022.

Katsam, wata ɗaya bayan wasiƙar, sai Emefiele ya ce wai ya haɗu da tsohon hidimin tsohon Shugaban Muhammadu Buhari, wato Sabiu Tunde a Fadar Shugaban Ƙasa, a ranar 6 ga Oktoba, 2023, wanda ya shaida masa cewa gara ma a sauya launin kuɗi.

“To a wannan ranar Gwamnan CBN ɗin ya rubuta wa Shugaba Buhari shawarar sauya launin kuɗi, kuma a ranar ce ya sa wa takardar hannun amincewa.

“Sai dai kuma Buhari ya bada umarnin a buga kuɗaɗen a cikin gida Najeriya. Sai dai kuma da aka tuntuɓi Kamfanin Buga Kuɗaɗen Najeriya, wato Nigerian Security Printing and Minting Plc, ya ce aikin zai ɗauki lokaci kafin ma a tsana sabon launin tukunna.

“Jin haka sai Emefiele ya kinkimi aikin ya kai shi Birtaniya, ya biya fam fam na Ingila har 205,000 ladar zana fallen hoton launin Naira 200, Naira 500 da Naira 1,000.” Wannan fa ba a kai ga maganar bugawa ba ma tukunna.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga wani ɓangare na binciken, inda Mai Binciken Musamman ya ce ya gano kawai Sauya Launin Naira da Emefiele ya yi, zamba da harƙalla ce kawai.

Mai Binciken CBN na Musamman, Obazee, ya bayyana a cikin rahoton binciken da ya gudanar cewa shirin sauya launin kuɗin da tsohon Gwamnan CBN, Goodwin Emefiele ya bijiro da shi, harƙalla ce kwai da zuma tantagaryar zamba.

Ya ce shirin ba a nemi amincewar Hukumar Gudanarwar CBN ba, kuma ba a nemi amincewa a rubuce daga shugaban lokacin ba, Muhammadu Buhari.

Ya ce hakan kuwa an kauce wa Sashe na 19 (1) na Dokar CBN, ta 2007.

“Kawai wata maƙarƙashiya ce Emefiele ya shirya domin damfarar ‘yan Najeriya, musamman manyan ‘yan siyasa. Kuma Emefiele ne ya shirya wannan zambar, shi da mataimakin sa a wancan lokacin, mai suna Folashodun Shonubi.

“Emefiele da Shinubi sun shirya zambar sauya launin kuɗi don su hana wasu manyan ‘yan siyasa kasa cimma burin su. To amma sai abin ya zama masifa da bala’in ƙuncin rayuwa ga ɗaukacin ‘yan Najeriya.”

Obazee ya ce CBN ya yi sabbin kuɗaɗen na N200, N500 da N1,000, kuma Naira bilyan 61.5 ya kashe wajen buga kuɗaɗen, waɗanda ya biya Naira biliyan 31.8 ga ɗan kwangilar. Kuma Naira biliyan 769,562 kaɗai na sabbin kuɗaɗen aka buga.

“Emefiele ya kwashi Naira 1,727,500,000 wai ya biya kuɗin lauyoyin biyo bayan shigar da CBN ƙara da aka yi ta yi, bayan ya sauya launin kuɗi.” Haka Obasee ya bayyana a cikin rahoton sa.

Share188Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Yadda zaku kaucewa haduwa da matsalar hakori

Next Post

Makarantar Madarasatu Anas Bin Malik Ta Yi Taron Yaye Dalibainta Sama Da 40 A Kaduna

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan
LABARAI

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

by aksam
May 4, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano
LABARAI

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

by Khadija Maitaya
May 4, 2026
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A  Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga  Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC
LABARAI

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC

by aksam
May 3, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Inna lillahi wa Inna ilayhi raji’un!!!

Inna lillahi wa Inna ilayhi raji’un!!!

May 10, 2025
Dalilan Kungiyar Kwadago na janye yajin aiki

Dalilan Kungiyar Kwadago na janye yajin aiki

June 4, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media