Yanzu-Yanzu: Kungiyar JIBWIS a Katsina ta kafa kwamitin da zai duba yarjejeniyar SAMÒA da gwamnatin tarayya ta sanya ma hannu
KungiyarJama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah JIBWIS reshen jihar Katsina karkashin jagorancin shugaban ƙungiyar na jihar Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan, ta kafa Kwamiti na masana wanda zai duba yarjejeniyar gwamnatin tarayya da SAMOA domin binciken abinda yarjejeniyar ta kunsa a matakin Jiha kamar yadda uwar Kungiya ta Kasa ta yi domin sanin martani da kuma matakin da kungiyar za ta dauka
Haka kuma kungiyar ta Izala ta ce ba za ta lamunci duk wani mummunan kuduri da zai saɓa ma dokokin addinin musu-lunci da kuma al’adun mutanen jihar Katsina
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta Katsina reporters ta samu cewa, kungiyar ta gudanar da taron Kafa kwamitin a masallacin G.R.A da ke Katsina inda aka tattauna muhimman batutuwa wanda za su fadada hanyoyin da’awa da ayyukan da Kungiyar ta sa gaba.










Comments 1