Babbar kotun tarayya da ke zama a Kano ta umurci gwamnatin jihar ta biya sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero diyyar Naira miliyan 10 saboda tauye masa hakki.
Wannan na zuwa ne bayan da mai shari’a Liman Mohammed ya bayyana cewa Alhaji Aminu Ado Bayero na da hurumin a saurari kararsa bayan ƙarar da ɗaya daga cikin masu naɗa sarki, Aminu Baba Dan Agundi ya shigar game da rikicin na masarautar Kano.
Alƙalin kotun, mai shari’a S. A. Amobeda ya ce matakin da jihar da jami’an tsaro suka ɗauka ya take hakkin walwala na Aminu Ado.
Lauyan mai kare sarkin Kanon na 15, Mamman Lawan Yusufari, ya ce umarnin da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar na kama Aminu Ado Bayero ba tare da madogara a shari’a ba, cin zarafinsa ne da take masa haƙƙi.
Mai shari’a Amobeda ya yanke hukuncin cewa umurnin da gwamnan ya bayar barazana ce kai tsaye ga ƴancin sarkin, kamar yadda yake a sashe na 35 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Kotun ta kuma tabbatar da cewa, tsarewar da aka yi wa Aminu Ado Bayero a gida ya saɓa wa hakkinsa na walwala, kamar yadda yake a sashe na 41(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Hukuncin da kotun ta yanke ya haɗa da hana waɗanda ake ƙara ci gaba da tsare Aminu Ado ko musguna masa.
Gwanatin Kano ta samar da dokar masarautar Kano ta 2024, tare da soke dokar masarautun Kano ta 2019, inda a dalilin haka aka sauke Aminu Ado daga kan mulki, sai dai ana ci gaba da shari’a a kotu kan lamarin.












