Hadimin gwamnan jihar Borno a ɓangaren harkokin al’umma, Cif Kester Ogualili ya hadu da ajalinsa
Hadimin gwamnan a bangaren yada labarai, Abdurrahman Ahmed Bundi shi ya tabbatar da hakan ga manema labarai
Gwamna Zulum ya mika ta’aziyya zuwa ga iyalan marigayin inda ya musu addu’ar jure wannan babban rashi da aka yi a jihar
Marigayin ɗan asalin jihar Anambra ne wanda ya fito daga karamar hukumar Dunukofia amma ya shafe tsawon rayuwarsa a jihar Borno.
“Ina bakin cikin sanar da ku cewa Hon. Kester Ogualili ya rasu, marigayin ya yi wa jihar Borno aiki tukuru wanda ya kasance mai son zaman lafiya kuma jakadan al’ummar Igbo.”
“Zamu ci gaba da tuna shi a matsayin wanda ya kawo hadin kai tsakanin al’ummar da ke rayuwa a jihar Borno.”









