Rahotanni daga Kaduna sun nuna cewa ƴan bindiga sun kai kazamin hari kauyen Angwar Danko da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari
Wakilin yankin a majalisar dokokin jihar, Yahaya Ɗan Salio, ya ce ya samu labarin har yanzun ƴan ta’addan ba su bar yankin ba
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Kaduna, Mansur Hassan, ya ce a saurare shi, zai fara tattara bayanai kafin ya ce komai
onarabul Yahaya Musa Dan Salio, wakilin Kakangi a majalisar dokokin jihar ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa har yanzu bai samu cikakken bayani ba dangane da adadin mutanen kauyen da aka sace amma ya tabbatar da cewa suna da yawa.
“Yanzu na samu kira daga yankin, inda aka sanar da ni cewa an yi garkuwa da mutane da dama.
“Ƴan bindigar sun kewaye kauyen, kuma a yanzu da muke magana suna can, suna kokarin tafiya da mutane zuwa cikin daji. Lamarin ya yi muni,” inji shi.












