Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da mai martaba Sarkin Bichi daga yin sabbin nade-nade da kuma daga likkafar wasu hakimai a masarautar.
Bayanin dakatar da nade-naden na kunshe ne a cikin wata wasika da ta fito daga ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu ta jihar kano mai kwanan watan 21 ga watan Fabrairu, mai dauke da sa hannun babban Sakataren ma’aikatar Ibrahim M Kabara.
Idan za’a iya tunawa masarautar ta Bichi ta shirya gudanar da nade-nade a yau Juma’a 1 ga watan maris na wannan shekarar ta 2024, Inda ta rubuta takardar neman sahallewar gwamnatin kano kafin aiwatar da nade-naden.
A ranar larabar data gabata ma ma’aikatar kananan hukumomi ta sake fitar da wata sanarwar, Inda ta sanar da dukkanin masarautun jihar kano da su dakatar da duk wani shirinsu na yin nade-nande ko daga darajar hakimai.
Sanarwa tace ana umartar dukkanin masarautun jihar da su tabbatar suna sanar da Ofishin kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi da al’amuran masarautu ta jihar kano duk wani lamari da ya shafi irin wannan batun.
Wasu dai na ganin wannan Mataki ba zai rasa nasaba da kallon hadarin kaji da ake zaton akwai a tsakanin masarautun Kano, Bichi, Rano, Gaya da Karaye da kuma gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf











