Daga Hassan Umar Gwammaja
Al’umma da dama ne Suka halirci gudanar da sallar jana’izar Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa ba tare da gawarsa ba bayan da ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da shi suka ƙi bayar da gawar tasa.
Haka kuma Ɗaruruwan mutane ne, suke ta yin Addu’o’in Allah Ata’ala ya bayyana wadda su ka kashe shi, bayan kammala Sallahr jana’izar a garin Sabon Birni da ke jihar Sokoto da yau Alhamis din nan.











