Sabuwar zanga-zaga ta barke a Calabar, babban birnin jihar Cross River, inda ma’aikatan gwamnati ke adawa da rashin biyan su albashi
Kamar yadda bidiyon zanga-zagar ya yadu, an ga yadda masu zanga-zagar suka mamaye ofishin sakataren gwamnatin jihar
Masu zanga-zagar sun ce har yanzu da watanni Fabrairu ya raba tsakiya ba a biya su albashi ba, yayin da suke kokawa kan tsadar rayuwa
Zanga-zagar ta barke ne tun a jiya Alhamis, 15 ga watan Fabrairu kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Ma’aikatan sun yi zuga tare da mamaye ofishin sakataren gwamnatin jihar, Mr. Anthony Owan Enoh.
A cewar masu zanga-zagar, yunwa na yunkurin ganin bayan su yayin da har watan Fabrairu ya raba tsakiya ba a biya su albashin watan Janairu ba.
Sai dai ofishin sakataren gwamnatin jihar ya nemi masu zanga-zagar da su rubuta korafi akan hakan a hukumance.
Bidiyon yadda ma’aikatan suka gudanar da zanga-zangar
Da ya ke wallafa bidiyon yadda zanga-zangar ke gudana, Anthony Ehilebo, wani ma’abocin kafofin watsa labarai ya ce:
“Kai tsaye daga birnin Calabar. Abin da ke faruwa a ofishin sakataren gwamnati kenan. Da alama Najeriya na dab da tarwatsewa. Tattalin arziki ya kara ta’azzara a wannan gwamnati.”









