Bitadakulli, an yi gidan kaso da sakataren jam’iyar PDP
Kotun Majistare a birnin Abakaliki da ke jihar Ebonyi ta tsare jigon PDP a gidan kaso kan zargin bata suna da karya
Ana zargin Chika Nwoba da aikata laifuka guda uku da suka hada da barazanar kisa da bata suna da kuma ba da bayanan karya
An gurfanar da Chika ne wanda shi ne tsohon kakakin jam’iyyar a jihar a yau Talata 13 ga watan Faburairu kan zarge-zargen
Kotun Magistare da ke birnin Abakaliki a jihar ita ta umarci tsare Chika a gidan gyaran hali bayan gurfanar da shi.
An gurfanar da Chika ne wanda shi ne tsohon kakakin jam’iyyar a jihar a jiya Talata 13 ga watan Fabrairu kan zarge-zargen.
Premium Times ta tabbata da cewa an kama Chika ne tun a ranar Lahadi 11 ga watan Faburairu bayan korafin da aka shigar a kansa.
Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar, Oguzor Offia-Nwali shi ya gabatar da korafi kan, Chika, a ofishin ‘yan sanda.
Nwali ya zargi Chika da wallafa wasu bayanai a shafin Facebook inda ya ke bata masa suna da cewa ya karkatar da wasu kudaden jihar.
Bayan neman belinsa Lauyan Chika ya ce laifin da ya aikata ya cancanci beli inda ya ce masu karar ba su samu amincewa daga kwamishinan shari’a a jihar ba.
Mai Shari’a, Lilian Ogodo ta umarci tsare shi a gidan kaso inda ta ce ya dace a gudanar da shari’ar ne a babbar kotun jihar, cewar Daily Post.










