Ganin wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomi 44 ya cika a jihar Kano, IPAC ta fara maganganu daga gefe.
Mai taimakawa IPAC a wajen harkokin shari’a, Salisu Umar ya tara manema labarai a ranar Talata, ya ce za a nada kantomomi.
Salisu Umar ya yi ikirari cewa Mai girma Abba Yusuf zai dauko wakilan da ya aika zuwa kananan hukumomin su karbe mulki.
Kwanaki gwamnatin Kano ta tura jami’ai uku zuwa kowace karamar hukuma da sunan za su yi aiki da shugabanni da aka zaba.
A ranar Laraba, jaridar Daily Trust ta ruwaito majalisar IPAC ta na cewa Abba Kabir Yusuf yana shirin nada kantomomi a jihar Kano.
Majalisar ta IPAC ba ta goyon bayan nadin kantomomin rikon kwarya a maimakon a shirya zabuka a kananan hukumomi 44.
Idan har gwamnatin Mai girma Abba Kabir Yusuf ba ta canza shawara ba, IPAC ta nuna a shirye ta ke da ta kai kara a kotu.
IPAC ta ce jam’iyyu 12 daga cikin 18 da ke da rajista a kasar suna goyon bayan ta a wannan barazana da take yi wa gwamnan Kano.
Da aka nemi jin ta bakin sakataren yada labarai na gwamna Abba Kabir Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fadawa ’yan jarida cewa za a nada shugabanni a duka kananan hukumomi.












Anawata gawata muje zuwa Abba kabir yusuf