Da sanyin safiyar yau Litinin ne wata mummunar gobara ta tashi a ofishin rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kano da ke Unguwar Nasarawa
Rahotanni sun bayyana cewa wani bangare na ofishin ‘yan sandan ya kone kurmus yayin da aka killace takardu da makamai
Kwamishinan’yan sandan jihar, CP Usaini Gumel ya sanar da hakan ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Abdullahi Haruna kyawa yana mai cewa an fara tantance takardun da abin ya shafa
“Da misalin karfe 05.45 na safe, hedikwatar ‘yan sanda ta kama wuta kuma wani bangare na ginin ya kone gaba daya.
“Wannan ya faru duk da kokarin da hukumar kashe gobara ta Jihar ta yi na shawo kan wutar.”
Gumel ya ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin faruwar lamarin, kamar yadda jaridar.
“Tuni aka killace yankin domin hana mutane shiga, hakazalika makamai da alburusai da ke ofishin suna nan inda suke.
“A halin yanzu babban jami’in ‘yan sanda na ofishin yana tantance wasu takardun da abin ya shafa.”
An tattaro cewa gobarar da ta tashi a ofishin provost, ta bazu zuwa sashen kudi, dakin taro, ofishin jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, ofishin mataimakan kwamishinan ‘yan sanda.
An kuma ruwaito cewa daukacin ofisoshin da ke saman bene na rundunar ‘yan sandan da aka gina a shekarar 1967 ne gobarar ta kone su, yayin da wutar ba ta shafi ofishin kwamishinan ‘yan sandan ba.









