DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
Najeriya ta lallasa Kamaru da ci 2-0 a gasar cin kofin Nahiyar Afirka na 2023 a yau Asabar.
Ademola Lookman ne ya zura kwallaye biyu a kowane rabin lokaci inda Najeriya ta samu nasarar
Yanzu dai ‘yan wasan Najeriyan za su kara da kasar Angola a wasan kusa da na karshe na gasar.
Tun da farko Angola ta lallasa Namibia da ci 3-0 a wasan da suka fafata a zagaye na 16.












