DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
Wani fusataccen matashi da aka bayyana sunansa da Sadiq Idrissu, ya kashe mahaifiyarsa a Jihar Adamawa, da ya bayyana cewa bai yi nadamar kisan gillar da ya yi mata ba.
Matashin dan shekaru 30, ya kashe mahaifiyarsa ne ranar 05/12/2023, a garin Boga cikin karamar hukumar Gombi a jihar, maimakon nadama kan kisan gillar da ya mata, amma cewa “ban yi nadamar kisan da na yi wa mahaifiyata ba” in ji matashin
Ya ci gaba da cewa “na kashe ta ne, saboda ta bayyana min ita mayya ce, da ma jama’a na zarginta da maita, kuma gaskiya ne, domin tana aikata wasu abubuwan mamaki, musamman da daddare.
“Mamana tana bayyana min a cikin mafarki a matsayin mayya, tana kuma jefa min tsoron da ke hana ni yin bacci da daddare” in ji matashin.
Ya ce ranar da abin ya faru “na dawo gidanmu cikin dare, sai ban same ta a dakinta ba, sai ‘yar uwata ke kwance, na shiga dakin babana ban same ta ba, saboda haka na fita neman ta a waje na same ta kuma nan take na harbe ta sau biyu, tunda na tabbata ita mayya ce” in ji shi.
Leadership ta ruwaito cewa Ita ma rundunar ‘yansandan jihar Adamawan ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ta tabbatar da lamarin, ya ce matashin ya kashe mahaifiyarsa bisa zargin ita mayya ce.
Ya ce bayan kammala bincike rundunar za ta gurfanar da matashin gaban kuliya.












