Kamfanin AEDC ya yi barazanar yanke wa fadar shugaban kasa wutar lantarki kan kuɗin wuta sama da naira biliyan 47 da yake bin su.
Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake na shugaba Tinubu ya yi murabus inda ya ce yunƙuri ne na karkatar da hankalin mutane.
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wata gawa tare da masu rakiyarta lokacin da aka yi jigilarta daga Legas zuwa Nsukka domin binne ta sun nemi miliyan 50 kudin fansa.
EFCC ta cafke wasu masu hakar ma’adanai a Ogun bayan bayanan sirri kan irin harkar da suke yi ta yi wa arzikin kasa zagon kasa.
Tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, ya kai kansa gaban jami’an EFCC.
‘Yan kasuwar magunguna ta Sabon Gari dake Kano sunyi zanga zangar lumana akan yunkurin tashin su zuwa Kasuwar Dangwauro.
Rahotanni daga ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja na cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe sama da mutum 12 tare da ƙona kimanin gidaje 30.
Dubban mutane sun hau kan titunan birnin Ibadan na jihar Oyo domin nuna fushinsu kan tsadar rayuwa.
Babban Kwandan Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Daurawa, yaje ofis inda yake kuma duba yadda al’amuran hukumar ke gudana hakan na zuwa ne bayan jita-jita da ta karade kafafen sada zumunta cewa ya ajiye aikinsa.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da kisan mutum 12 a Kajuru.
Hukumar NAFDAC ta rufe wasu kamfanonin haɗa giya a Jihar Filato saboda gaza bin ƙa’idojin sarrafa giyar da kuma haɗa giya ta leda ta kimanin miliyan 6 wadda aka haramta samar da ita.
An fara sabunta ginin Masallacin Juma’ar Zariya da a baya ya rufta har ya yi sanadiyar mutuwar mutane 8 da jikkatar wasu da dama.
Kungiyar masu sarrafa siminti sun yi alkawarin daidaita farashin kaya kungiyar ta ce daman sun hango wannan matsalar kuma sun yi gargadi amma ba a ji ba.
‘Yan takarar Senegal sun yi kira da a kaɗa kuri’a cikin makonni shida.
Sojojin ruwan Maroko sun ceto baƙin haure ƴan Afirka 141.











