DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Jaridar Aksam Media a ranar Laraba cewa Akeredolu ya mutu a Legas.
Majiyar ta kuma gano cewa likitocin fadar gwamnatin jihar ne ke kula da shi har zuwa rasuwarsa saboda ba za su iya kai shi kasar waje ba.
“Akeredolu ya mutu; ya rasu ne a Legas Yana da shekaru 67 a duniya.,” inji majiyar.
Gwamnan da ke fama da rashin lafiya ya dawo Najeriya a cikin watan Satumba bayan hutun jinya na watanni uku a kasar Jamus, kuma a kwanan baya ya ci gaba da wani taron bayan da shugaba Bola Tinubu ya umarce shi da ya mika mulki ga mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa.
Mataimakin sa, Aiyedatiwa ya tsaya a matsayin mukaddashin gwamna.
Bayan dawowarsa Najeriya a watan Satumba, Akeredolu ya zauna a Ibadan, babban birnin jihar Oyo inda ya yi kokarin gudanar da mulkin jiharsa daga can, lamarin da ya janyo cece-ku-ce tsakanin jama’a.











