Shugaban Kasar Burkina Faso, Kaptin Ibrahim Traoré ya ƙi aminta da tayin Amurka na tura masa ’yan gudun hijira da ba bisa ka’ida ba zuwa Burkina Faso.
Amurka ta nemi Traore ya karɓi ’yan Afrika da ba ’yan Afrika ba da ta kora daga ƙasarta zuwa ƙasar Burkina, amma Kapitan Traoré ya ƙi aminta da buƙatar Amurka.
Ya jaddada cewa Burkina Faso ƙasa ce mai mutunci, da ’yanci da ɗaukaka, ba wurin aika waɗanda aka kora ba.
Duk da haka, a cikin ruhin ’yan’uwantakar Afirka, Kapitan Ibrahim Traoré ya bayyana cewa duk wani Baafrike da ke zaune a Amurka kuma yake son dawowa da kansa zuwa ƙasar mutanen nagarta, za a ba shi bisa kyauta ba tare da sharadi ba.
A nata martanin, Amurka ta sanya takunkumin visa ga ’yan Burkina Faso da ke son shiga ƙasarta.










