Kungiyoyin kwadago a Najeriya NLC da abokiyar ta ta TUC sun bayyana dakatar da yajin aikin da suka fara a fadin kasar bayan zaunawa da gwamnatin tarayya.
Kungiyoyin sun ce dakatarwar ta biyo bayan tsoma bakin da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya yi.
Zaman wanda aka fara shi da misalin karfe bakwai na Daren Alhamis 15/11/2023, ya dauki kimanin sa’a guda, inda kungiyoyi daban-daban suka yi tsokaci a kan sakamakon taron da shugabannin kungiyoyin kwadago da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu .
Kungiyoyin sun tsunduma yajin aikin ne biyo bayan cin zarafin da suka ce rundunar yan sanda ta yiwa Shugaban su Joe Ajaero a jihar Imo.












