• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Wasu fasinjojin jirgin sama sun sha da kyar bayan sun hadu da hadari

aksam by aksam
July 13, 2023
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
469
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Jirgin saman samfurin E-120, mallakar kamfanin jiragen sama na Halla Airlines ya taso ne daga birnin Garoowe na yankin Puntland na Somaliya zuwa filin jirgin saman Aden Adde na Mogadishu ya hadu da iftila’i na hadari a kan hanya.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Somaliya tace an sami nasarar tserar da dukkan fasinjoji 30 da ma’aikatan jirgin su hudu.

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

“Babu rasa rayuwa a hadarin sai dai kananan raunuka,” in ji hukumar SCAA a cikin wata takaitacciyar sanarwa. “Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman ta Somalia ta tabbatar da cewa za’a fitar da rahoton farko a kan hadarin da zarar an kammala binciken da ake yi a yanzu.”

Hotunan da aka yadda ta talabijin ya nuna jirgin ya kauce daga titin tashi da saukar jirage ne nan take bayan ya sauka.

Matukin jirgin bai bayar da rahoton wata matsala ba ga hasumiyar kula da zirga-zirgar jiragen sama kafin faruwar lamarin.

Ismail Mohamud na kamfanin jiragen sama na Halla ya shaidawa Muryar Amurka cewa daga baya za’a fitar da rahoton sakamakon binciken.

Alamu na farko sun nuna cewa mai yiwuwa kuskuren matukin jirgin ne ya haddasa hadarin, a cewar wani jami’in Somaliya da ya bukaci a sakaye sunansa.

Ya kara da cewa “Za a tabbatar da gaskiyar lamarin da zarar an yi nazarin na’urar nada murya da akwatin bayyana bincike na cikin jirgi.”

Hukumomin filin tashi da saukar jiragen sama na Somalia sun inganta ayuka a cikin ‘yan shekarun nan, inda suka sake karbe ikon zirga-zirgar jiragen sama daga Majalisar Dinkin Duniya. A farkon wannan shekarar, Somaliya ta dawo da matsayinta na ajin farko daga kungiyar sufurin jiragen sama ta kasa da kasa.

Jirage sama da 150 na cikin gida da na ketare ne ke amfani da filin jiragen sama na Mogadishu a kullum, a cewar hukumar kula da filayen jiragen sama. Manyan kamfanonin jiragen sama na kasa-da-kasa da ke amfani da filin jirgin sun hada da Turkish Airlines, Qatar Airways da Ethiopian Airlines.

Share188Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Yadda sanata Lado Danmarke ya gwangwaje wasu mazabu da ayyukan ci-gaba

Next Post

Daurawa ya bayyana matakai da irin kayan Dakin da zasu rabawa zawarawa da yanmata bayan Hizba ta d’aura musu Aure

aksam

aksam

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa  ƴar Tik-tok  Dake Unguwar  Ɗanbare A Jihar Kano
LABARAI

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

by aksam
June 20, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

by Khadija Maitaya
June 19, 2026
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka
LABARAI

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

by Khadija Maitaya
June 16, 2026
China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI
LABARAI

China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI

by Khadija Maitaya
June 14, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato

Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato

June 2, 2026
A shirye muke wajen ganin kananan hukumomi sun dawo cikin hayyacinsu,

Gwamnan Kano Ya Turawa Majalisar Dokoki Sunayen Kantomomi 44 Domin Tantancewa

March 5, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media