Mujallar Forbes da ta saba bibiyar masu arziƙi na duniya, ta ruwaito cewa a yanzu hamshaƙin biloniyan nan ɗan ƙasar Afirka ta Kudu, Johann Rupert shi ne mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka.
Hakan na nufin Johann Rupert mai shekara 73, ya kere attajirin ɗan kasuwa na Najeriya wanda a baya yake riƙe da matsayin.
A alƙaluman da Forbes ta fitar na baya-bayan nan, a kan arzikin attajirai a kowacce rana, darajar arzikin Johann Rupert ta kai dala biliyan 10, yayin da Aliko Dangote aka ƙiyasta nasa arzikin a kan dala biliyan 9.7.
Aliko Dangote, mai shekara 66, ya koma mataki na biyu a jerin masu arzikin Afirka bayan da dukiyarsa ta yi ƙasa daga dala biliyan 13.5 zuwa dala biliyan 9.5 a farkon shekarar 2024.
Mujallar ta nuna cewa an samu raguwar kuɗin hamshaƙan ƴan kasuwa kamar Rabiu Abdussamad da darajar arzikinsa ya kai dala biliyan 5.7 da Mike Adenuga wanda nasa arziƙin ya kai dala biliyan 3.1.
Bayanai na cewa raguwar darajar arzikin nasu, ba zai rasa nasaba da yadda darajar naira ke ci gaba da faɗuwa ba, da kuma wasu matsaloli da suka shafi tattalin arziki.










