Tsohon kakakin Majalisar Tarayya, Hon. Yakubu Dogara ya fadi yawan alawus da ake ba shi.
Dogara ya ce kwata-kwata albashinsa bai wuce N400,000 ba lokacin da ya shugabanci Majalisar.
Tsohon kakakin Majalisar ya kuma bayyana cewa ana ba shi alawus na N25m ne a lokacin.
Ya ce fayyace hakan ya zama dole ganin yadda mutane suke zaton makudan kudi ƴan Majalisar ke samu a banza, cewar jaridar Channels TV.
“Lokacin da na ke kakakin Majalisar Tarayya, ana ba ni albashin N400,000 a wata da kuma alawus na N25m.”
“Na umarci mai kula da kudi na ya bude wani asusun daban domin zuba kudin alawus saboda na al’umma ne wannan.”
“Ya yi mun korafi cewa mutane suna yawan roko sai na ce masa idan kudin suka kare ya ci ba shi, idan wasu sun shigo sai ka maye gurbinsu da shi.”











